SiyasaFaransa
Zubar da ciki a Faransa zai shiga cikin kundin tsarin mulki
March 4, 2024Talla
Wakilaina 'yan majalisar dattijai na shirin kada kuri'a da gagarumin rinjaye domin amincewa da gyaran kundin tsarin mulkin da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta gabatar. Masu adawa da zubar da cikin sun ba da sanarwar yin wani gangami a Versailles, yayin da magoya bayan sauye-sauyen zasu yi taro a Trocadéro da ke a birnin Paris domin nuna farincikinsu. Hakan dai na zuwa ne kwanaki hudu kafin ranar takwas ga Maris, ranar mata ta duniya.