1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lateefa Mustapha Ja'afar MA
November 23, 2018

Jaridar Neues Deutschland ta ce shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya samu mafita yayin ziyararsa a Afirka ta Kudu. Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudun na fatan Jamus ta zuba jari a kasar.

https://p.dw.com/p/38nE7
Bundespräsident Steinmeier in Südafrika
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Za mu fara da jaridar Neues Deutschland wadda ta rubuta sharhinta mai taken ''Steinmeier na son Afirka ta Kudu ta zamo kawar Jamus a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya''

Ziyarar Steinmeier dai na zuwa ne watannin kalilan bayan da aka tilastawa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma sauka daga mukaminsa sakamakon zarge-zargen cin hanci da rashawa, inda ake wa ziyarar kallon ta lokacin da ya dace Jamus ta sabunta da dangantakar da ke tsakaninta da Afirka ta Kudu. Frank-Walter Steinmeier ya samu rakiyar wakilan ‘yan kasuwa, wanda hakan ya zo a kan gaba domin kuwa Afirka ta Kudu na neman masu zuba jari ruwa a jallo, yayin da a hannu guda hakan ke tamkar mafita ga Steinmeier wanda bai yi kasa a gwiwa ba wajen gabatar da tawagar 'yan kasuwar da tai masa rakiya. 

Niederlanden - Den Haag - Prozess Kriegsverbrechen - Alfred Yekatom
Hoto: Reuters/P. van de Wouw

Ita kuwa jaridar die tageszeitung, ta rubuta sharhinta ne kan jagoran 'yan tawayen Anti Balaka na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Alfred Yekatom da aka fi sani da Rambo, wanda aka mika gaban kuliya. A sharhin nata mai taken: "An tsare Rambon Bangui a birnin The Hague"

 

Ta ce a karon farko Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na mika jagoran ‘yan tawaye ga kotun kasa da kasa da ke hukunta masu aikata manyan laifuka. Alfred "Rambo" Yekatom shi ke da alhakin kisan kiyashi ga Musulmi kuma zai gurfana a gaban kotun kasa da kasa mai hukunta masu aikata manyan laifuka a birnin Hague bisa zargin kisan fararen hula yayin yakin basasar da ya barke a Jamhuriyar Afirka ta Kudu daga shekara ta 2013 zuwa 2014. Tuni dai aka tsare shi sakamakon wasu dalilai, inda kungiyoyin fafutukar kare hakkin dan Adam ke yabawa da matakin.

 

Rückkehrerappell Kampfhubschrauberregiment 36
Hoto: picture-alliance/dpa/S.Stein

A karshe sai sharhin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta mai taken ''Kare zaman lafiya, kashe masu kaifin kishin addini'' Jaridar ta ce a yankin Gao na kasar Mali, dakarun Faransa da Jamus na aiki kafada-da-kafada. Ta ce kiris ya rage Mali ta zamo tarihi, tuni bakaken tutocin 'yan ta’adda masu da’awar jihadi ta mamaye arewacin kasar. Sun rusa wuraren adana tarihi na Timbuktu haka ma Gao. A hannu guda kuma Faransa na ganin su ke da iko da yankin. Ofishin dakarun Jamus a Faransa ya bayar da rahoton yadda sojojin Faransa ke farautar masu kaifin kishin addinin a yankin Sahel. A yanzu sojojin kasashen biyu sun hada karfi waje guda.