Ziyarar Kerry a Masar ta gamu da boren ′yan adawa | Labarai | DW | 02.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Kerry a Masar ta gamu da boren 'yan adawa

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kery na wata ziyara a Masar inda ya ke cin karo da zanga zanga da kuma kiraye kirayen yin watsi da shi.

Masu adawa da gwamnatin kasar mai kishin Islama da Mohammed Mursi ke wa jagora suka kira wannan zanga-zanga a gaban ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar da kuma ofishin jakadancin Amirkar da ke birnin Alkahira, domin nuna adawa da goyon bayan da gwamnatin jam'iyyar 'yan uwa Musulmi ke samu daga Amirka duk da fatali da take yi da tsarin demokradiyya.

An samu rahotannin da ke nuni da cewa kusoshin adawa guda biyu, wato Hamdien Sabahi da ya taba tsayawa takarar zaben shugaban kasa da Mohamed al Baradei da ya taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel sun ce ba za su gana da John Kerry kamar yadda aka bukata ba. Sakataren harkokin wajen na Amirka zai gana ne da shugaba Mursi da kuma wasu kusoshin siyasar kasar yayin ziyarar tasa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal