Ziyarar Bush a kudancin Asiya | Labarai | DW | 01.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Bush a kudancin Asiya

Shugaban kasar Amurka George Bush,ya fara ziyarar kwanaki 4 zuwa kudancin Asiya.

Kafin ya bar birnin Washington dai sai da Bush yayi kira ga kasar Pakistan da ta kara kokarin da takeyi wajen yaki da taaddanci.

Ana sa ran a yau laraba Bush zai isa babban birnin kasar India,wato new Delhi,daga nan kuma zai kai ziyara zuwa kasar pakistan .

Ganawar da zai yi da Firaministan India Manmohan Singh da shugaban kasar Pakistan Parevez Musharraf,Bush yana fatar inganta hadin kai a fannin makamashin nukiliya tsakaninsu.

Bush yace zai kuma tunatarwa da shuagan Pakistan cewa,suna fuskantar abokin gaba daya a fuskar taaddanci,wato Osama bin Laden.

Cikin wata hira da akayi da shi kafin tafiyar tasa,Bush ya amince cewa Musharraf yana fuskantar matsalolin siyasa a cikin gida sakamakon goyon bayansa ga yaki da taaddanci na Amurka.

A yau din nan masu zanga zanga da suka fara tun jiya talata suna ci gaba da zanga zanga rakan titunan birnin Mumbai game da wannan ziyara ta Bush.