Ziyarar Assad a Rasha | Labarai | DW | 22.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Assad a Rasha

Kasar Rasha ta kara fitowa fili don tabbatar da matsayinta na wanda ke da fada aji don warware rikicin Siriya bayan ganawar shugabannin kasashen biyu

Ana dai ci-gaba da yin tsokaci bisa ziyar ta ba zata da shugaban kasar Siriya Bashar Al-Assad ya kai kasar Rasha a jiya Laraba. Wanda shi ne karon farko da Assad ya fita kasar tun bayan shekaru biyar da fara yakin basasa a Damaskus. A ziyar Bashar Al-Assad ya gana da takwaransa Vladimir Putin inda suka tattauna rikicin Sirya da ma tallafin da Rasha ke bai wa gwamnatinsa. Amirka wanda ke marawa 'yan tawayen Siriya baya don kifar da gwamnatin Assad, ta soki irin tarbar girmamawa da karamcin da Rasha ta yi wa Assad yayin ziyarar.