Ziyara Salim. A. Salim a Darfur
August 27, 2007Talla
Wakilin ƙungiyar taraya Afrika, a rikicin Darfur Salim Ahmed salim, ya yi kira ga ɓangarori daban-daban masu yaƙar juan a yankin Darfur na ƙasar Sudan da su tsagaita wuta.
Ahmed Salim, yayi wannan kira a garin Zalengei, ma´aifar Abdel Wahed Mohamed Nur, shugaban rundunar tawayen SLM, wadda ta ƙauracewa taron da ya haɗa ƙungiyoyin tawayen Darfur, a birnin Arusha na ƙasar Tanzania.
A yau wakilin AU, zai ci gaba da wannan rangadi a Darfur, inda zai gana da yan gudun hijira na yankin Zalengei.
Wannan ziyarci-ziyarce, na matsayin shiri, ga tura rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Ɗinkin Dunia, a wannan yanki na Darfur, da ke fama cikin tashe-tashen hankula.