Ziyara Havier Solana a kasar Jordan
November 14, 2005Talla
Sakataran harakokin wajen kungiyar gamaya turai Havier Solana ya kai ziyara aiki a kasar Jordan, domin issar da ta´aziyya, bayan haren haren kunar bakin wake da su ka abkawa kasa,r wanda kuma su ka yi sanadiyar mutuwar mutane 57 ranar laraba da ta wuce.
A ganawar da yayi da Sarki Abdallah, Havier solana, ya shaida masa hadin kan EU ga yunkurin yaki da ta´adanci a dunia.
A karshen ziyara ta Jorda,Havier Solana ya ci gaba zuwa Israela da Palestinu, domin tantanna batun zaman lahia a yankin gabas ta tsakiya, tare da hukumomin wannan yankuna.