Ziyara Havier Solana a Jamhuriya Demokradiyar Kongo | Labarai | DW | 19.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Havier Solana a Jamhuriya Demokradiyar Kongo

Shima Sakataren harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai, Havier Solana, ya kai ziyara aiki a Jamhuriya Demokaraɗiyar Congo.

A tsawan kwanaki 2, Solana zai tantana da shugaban ƙasa Lauran kabila, da da sauran masu faɗa a ji a fagen siyasar ƙasar, na ɓangaren adawa da masu mulki.

Ya kai wannan ziyara a shirye shirye tura dakarun ƙungiyar gamayya turai, domin tabatar da tsaro a zaɓen da za a shirya, a watan juni na shekara bana.

Ministocin harakokin tsaro, na ƙunguiyar Eu, su ka umurci Havier Solana, ya kai wannan ziyara ta gani da ido, domin tsaida matakan aika dakarun.

A baki daya sojoji dubu daya a ke sa ran kungiyar gamayya turai z ata aika a yankin na tsakiyar Afrika da ke fama da rigingimun tawaye.

Ranar litinin mai zuwa, ministocin harakokin wajen EU za su zamann taro a birnin Brussels, domin cimma matsaya ɗaya a game da wannan batu.