Zimbabuwe: ′Yan sanda sun tarwatsa zanga-zangar adawa | Labarai | DW | 12.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabuwe: 'Yan sanda sun tarwatsa zanga-zangar adawa

Jami'an tsaron birnin Harare sun yi amfani da kulake wajen tarwatsa wata zanga-zanga da 'yan adawar kasar suka shirya domin nuna rashin amincewarsu da nadin jami'an hukumar kula da aikin rajistan masu zabe.

'Yan sanda a birnin Harare na Zimbabuwe sun yi amfani da kulake da barkonon tsohuwa da ma ruwan zafi wajen tarwatsa wata zanga-zanga da 'yan adawar kasar suka shirya domin nuna rashin amincewarsu da nadin jami'an hukumar kula da aikin rajistan masu zabe da suke zargi da kasancewa 'yan amshin shatar Shugaba Mugabe.

Tuni dai jam'iyyar adawar ta MDC ta yi tir da Allah wadai da abin da ta kira amfani da karfin da ya wuce kima da 'yan sandan suka yi wajen murkushe zanga-zangar da adawar ta ce ta lumana. 

Yau watanni da dama kenan da 'yan sanda ke yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe zanga-zangar yau da kullum da kungiyoyin farar hula na Zimbabuwen suka kaddamar a biranen kasar da dama, domin nuna adawarsu da aniyar Shugaba Mugabe mai shekaru 93 da ke kan karagar mulkin kasar tun a sjhekara ta 1980 ta sake tsayawa takarar a zaben da kasar za ta shirya a shekara ta 2018.