Zimbabuwe: Shugaba Mugabe zai gana da sojoji | Labarai | DW | 19.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabuwe: Shugaba Mugabe zai gana da sojoji

Shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe wanda da dama daga cikin magoya bayansa suka juya masa baya na shirin ganawa a wannan Lahadi da shugabannin sojojin da suke tsare da shi a gidansa tun 'yan kwanakin da suka gabata.

Shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe wanda da dama daga cikin magoya bayansa suka juya masa baya na shirin ganawa a wannan Lahadi da shugabannin sojojin da suke tsare da shi a gidansa, a yayin da a share daya kwamitin gudanarwa na jam'iyyarsa ta zanu PF zai gudanar da taro a wannan rana domin bayyana matsayinsa a game da makomar Shugaba Mugabe. 

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan kasaitacciyar zanga-zangar neman shugaban ya sauka daga mulki da 'yan kasar suka shirya a biranen Harare da Bulawayo birnin na biyu mafi girma a kasar, zanga-zangar da kuma ta samu halartar 'ya'yan jam'iyyar Zanu PF ta Shugaba Mugabe da magoya bayan 'yan adawa har ma da wasu fararen fata na kasar. 

A lokacin zanga-zangar da ta gudana a jiya a birnin Harare masu zanga-zanga sun yi yinkurin yin tattaki zuwa fadar shugaban kasa, amma sojojin kasar suka taka masu birki.