1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Mugabe ya yi burus da kiran majalisa

Gazali Abdou Tasawa
May 28, 2018

Tsohon Shugaban Zimbabuwe Robert Mugabe ya sake yin burus da gayyatar da majalisar dokokin kasar ta yi masa na ya bayyana a gabanta domin bayar da bahasi kan batan wasu kudade na cinikin lu'u-lu'u.

https://p.dw.com/p/2yTzx
Simbabwe Robert Mugabe 2017, Präsident
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

Tsohon shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe ya sake yin burus da gayyatar da majalisar dokokin kasar ta yi masa na ya bayyana a gabanta domin bayar da bahasi kan batun batan dabon wasu kudade na dalar Amirka miliyan dubu 15 na lu'u-lu'u da kasar ta sayar a lokacin mulkinsa a shekara ta 2016. 

Shugaban kwamitin kula da harakokin ma'adanai a majalisar dokokin kasar ta Zimbabuwe Temba Mliswa ya ce sun yi ta zaman jiran zuwan tsohon shugaban a wannan Litinin amma bai bayyana ba sai dai ya ce za su sake aika masa da wata gayyatar a rubuce. 

Da ma dai a makon da ya gabata tsohon shugaban ya yi burus da kiran da majalisar dokokin ta yi masa. A shekarar da ta gabata ne wani rahoton Kungiyar Global Witness ya zargi Robert Mugabe da karkatar da akalar kudaden lu'u lu'un domin cimma wasu manufofinsa na siyasa musamman na murkushe abokan hamayyarsa.