Zimbabuwe: Gawar Mugabe ta isa gida | Labarai | DW | 11.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabuwe: Gawar Mugabe ta isa gida

Gawar tsohon shugaban kasar zimbabuwe marigayi Robert Mugabe ta isa Harare babban birnin kasar cikin rakiyara dakarun soja.

Bildergalerie Robert Mugabe Simbabwe Afrika (picture-alliance/dpa)

Tsohon shugaban kasar Zimbabuwe marigayi Robert Mugabe

Matar mamacin Grace Mugabe cikin babaken kaya da shugaban kasar Emmerson Mnangagwa na daga cikin dimbin mutanen da suka halarci filin sauka da tashin jiragen sama na kasar, domin tarbar gawarsa. Da yake jawabi ga mutanen da yawansu ya kai 1,000 da suka je tarbar gawar Mugaben, Shugaba Mnangagwa ya bayyana Mugaben a matsayin jagoran juyin-juya halin kasarsu. Rahotanni sun nunar da cewa za a nuna gawar tsohon shugaban da ya kwashe shekaru 37 yana mulki a Zimbabuwen a wuraren tarihi, kafin a binne shi a ranar Lahadi mai zuwa a wani gurin da har yanzu ba a bayyana ba, abin da ke nuna akwai wata a kasa tsakanin iyalan stohon shugaban da gwamnati. Mugabe dai ya rasu ne a ranar Jumma'ar makon da ya gabata, a wani asibiti da ke kasar Singapor yana da shekaru 95 a duniya.