1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harare: EU na shakkun sakamakon zabe

Yusuf Bala Nayaya
August 1, 2018

Masu sanya idanu a zaben kasar Zimbabuwe daga Kungiyar Tarayyar Turai sun soki yadda aka gaza kammala bayyana sakamakon zaben kasar da suka bayyana da cewa "babu dalilin tsaikon bayyanawa".

https://p.dw.com/p/32RKL
Simbabwe Wahl | Anhänger von MDC
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Hakan dai na zuwa ne yayin da daga bangaren 'yan adawa suke zargin an tafka magudi daga bangaren hukumar zabe da ma jam'iyyar ZANU-PF mai mulki.

Masu sa idanun daga EU sun bayyana rashin gamsuwa da yanayi na siyasar da ma rashin aminta da yadda harkokin bayyana sakamakon ke gudana. Kawo yanzu dai jam'iyyar ZANU-PF mai mulki ta samu kashi biyu bisa uku na kujerun majalisa. Shugaba Emmerson Mnangagwa na ZANU-PF ya yi mamaya a yankunan karkara yayin da babban dan adawa na jam'iyyar MDC Nelson Chamisa ya samu goyon baya a yankunan birane. Hukumar zaben kasar ta Zimbabuwe dai ta bayyana cewa sai a ranar Alhamis ne za ta fara bayyana sakamakon zaben shugaban kasa ganin yadda korafe-korafe suka yi yawa daga jam'iyyu da ke cikin zaben.