1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Bore kan zargin magudin zabe

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
August 1, 2018

Zanga-zangar adawa da rashin bayyana sakamakon zabe a Harare babban birnin kasar Zimbabuwe ta rikide ya zuwa mummunan tashin hankali.

https://p.dw.com/p/32TKs
Simbabwe, Harare: Anhänger der Opposition Chamisas MDC-Partei protestieren auf der Straße
Hoto: Reuters/S. Sibeko

Matasa magoya bayan jam'iyyar adawa ta MDC sun bazu a kan titunan birnin Harare domin nuna kin amincewarsu da sakamakon farko da ke nuna cewa jam'iyya mai mulki ta ZANU-PF ce ke kan gaba a zaben 'yan majalisun dokoki, tare kuma da nuna rashin amincewarsu da jan kafa da hukumar zaben kasar ZEC ke yi wajen bayyana sakamakon zaben shugaban kasa.

Jami'an tsaro da suka hadar da sojoji da 'yan sanda sun fesa ruwan zafi da kuma harsasai a kan matasa masu zanga-zangar da ke tunkarar ofishin hukumar zaben na Zimbabuwe. Rahotanni sun nunar da cewa akalla mutum daya ya rasa ransa a wannan zanga-zangar yayin da wani jigo a babbar jam'iyyar adawa ta MDC, Tendai Biti ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA cewa mutane biyu ne suka rasa rayukansu. An dai jiyo daga cikin masu zanga-zangar na cewa.

"Ina zanga-zanga ne saboda ba wannan sakamakon muka zaba ba, abu na biyu kuma me yasa suke jan kafa wajen sanar da sakamakon zaben shugaban kasa? Abin da suka yi ke nan a shekara ta 2008, abin da muke bukata shi ne mu san sabon shugabanmu."

Simbabwe, Harare: Anhänger der Opposition Chamisas MDC-Partei protestieren auf der Straße
Hoto: Reuters/S. Sibeko

Wannan kuwa cewa yake: "Mun zo nan don muna son a ji kokenmu. Ba ma son abin da hukumar ZEC ke yi, suna sace mana kuri'u, mun san abin da muka zaba, ba ma son wadannan shugabannin, muna bukatar shugabanni na gari."

Shakku kan sakamakon zaben

Wannan dai shi ne karon farko da al'ummar Zimbabuwe suka gudanar da zabe ba tare da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe da ya kwashe tsawon shekaru 37 yana mulki a kasar ba. Ko da yake masu sanya idanu na kungiyar Tarayyar Turai sun nunar da cewa akwai fargabar gwamnati za ta yi kaka-gida a batun sanar da sakamakon zaben, wanda ake ta samun tsaiko. Sai dai sun nunar da cewa an samu ci gaba, kamar yadda Elmar Brok jagoran tawagar masu sanya idanun daga kungiyar Tarayyar Turan ke cewa.

"An samu ci gaba sosai idan aka hada da zabubbukan baya da suka gudana, sai dai ko za a iya kiransa sahihin zabe mai inganci? Wannan ne ba ni da tabbas a kai."

Kira da a kwantar da hankali

Simbabwe, Harare: Die Polizei eröffnet das Feuer gegen Demonstranten
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Rahotanni sun nunar da cewa jami'an 'yan sanda ne suka bukaci da a tura sojoji su taimaka musu wajen dakile zanga-zangar. Amma a lokacin da take jawabi dangane da tura sojoji wajen da ake gudanar da zanga-zangar, ministar shari'a ta kasar Ziyambi Ziyambi ta ce an tura su ne  domin su tarwatsa dandazon masu zanga-zangar su kuma tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda da kuma tsaro.

A nasa bangaren Shugaba  Ermason Mnangagwa ya bukaci al'ummar kasar da su kwantar da hankalinsu a shafinsa na Twitter, yana mai cewa tilas su nuna hakuri da juriya da kuma yin abin da zai kare al'umma.