Zimbabuwe: An yi jana′izar Tsvangirai | Labarai | DW | 20.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabuwe: An yi jana'izar Tsvangirai

A wannan Talatar ce (20.02.2018) aka yi jana'izar madugun 'yan adawan kasar Zimbabuwe marigayi Morgan Tsvangirai a kauyensu na Buhera da ke gabashin kasar.

An dai samu halartar dubban magoya mayansa, da jami'an diflomasiyya da kuma shuganannin siyasa. Da yake magana shugaban riko na jam'iyyar MCD ta marigayi Tsvangirai, Nelson Chamisa, ya ce wannan taro, taro ne mai cike da tarihi, domin sun raka gwarzon maza ya zuwa gidansa na karshe:

"Lalle mun binne gawarsa, amma kuma bamu binne akidarsa ba. Domin zamu dawo da akidarsa musamman ma ta samar da tsari na Demokradiyya wanda zai yi aiki dakowa da kowa, akida ta mutunta incin al'ummar, akida ta cikakar Demokaradiyya."

Madugun 'yan adawan kasar ta Zimbabuwe mai shekaru 65 da haihuwa, ya rasu ne a makon da ya gabata a kasar Afirka ta Kudu, inda ya kwanta a Asibiti domin jinya. Sai dai kuma ya bar jam'iyyarsa a matsayin marainiya ganin yadda take fama da tarin matsaloli na cikin gida.