Zika na iya haddasa illa ga kwakwalwar dan Adam | Labarai | DW | 18.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zika na iya haddasa illa ga kwakwalwar dan Adam

Masu yin bincike kimiyya da masana sun ce cutar zika na iya yin mummunar illa ga kwakwalwar dan Adam,bayan nakasar da take haddasawa ga jariran da akan haifa idan har ta harbi mace mai juna biyu.

Masu yin binciken sun yi gwaji ne a kan kwakwalwar bera wanda gwajin ya nuna cewar Zikar na iya haddasa barna mai yawan gaske ga kwakwalwar dan Adam.Masanan sun yi gargadin cewar cutar ta Zika na iya rikidewa a gaba ta rika yin bugon biyu ga macen da ke dauke da juna biyu da kuma dan da za ta haifa.