Zargin magudi a zaben Gini
October 12, 2015Duk 'yan adawan da suka tsaya takarar neman shugabancin kasar Guinea, su bakwai, wadanda kuma suka kalubalanci shugaba mai ci Alpha Conde sun yi kira da a soke zaben bisa zargin tabka magudi.
Wannan furuci na su ka iya janyo fargaba a wannan kasar da ta yi kaurin suna wajen rikicin bayan zabe musamman irin na kabilanci.
Conde wanda ya hau karagar mulki bayan juyin mulki, ya sami magoya baya sosai a zaben ranar lahadi sai dai wata kila ratan da ya ba abokan hammayarsa ba zai yi tazarar sosai ba ta yadda sai an je zagaye na biyu a zaben.
'Yan adawan dai a karkashin jagorancin madugun su Cellou Dalein Diallo sun fadawa wani taron manema labarai cewa akwai magudi da kura-kurai da dama, inda ya kwatanta cewa, akwai yankunan da basu ma sami katin zabe ba duk da cewa an yi musu rajista