Zargin illata Lula da Silva a siyasance | Labarai | DW | 15.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin illata Lula da Silva a siyasance

Tsohon shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya ce zargin da ake masa kan cin hanci da rashawa wata kullalliya ce da aka shiryo da nufin yi masa illa a siyasance.

Mr. Da Silva na wadannan kalamai ne bayan da masu gabatar da kara suka ce shi ne ya jagoraci wasu jami'an gwamnati wajen badakalar cin hanci da rashawa da aka tafka a kamfanin man kasar wato Petrobras. Tsohon shugaban wanda ke dasawa da Dilma Rouseff da aka tsige daga mukaminta na shugabancin kasar ya ce an shirya wannan abu ne don ganin tauraruwarsa ta dusashe kafin zaben gama-gari da za a yi a kasar cikin shekarar 2018.