Zanga-zangar ′yan adawa a Brazil | Labarai | DW | 03.10.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar 'yan adawa a Brazil

Dubban magoya bayan 'yan adawa a Brazil sun gudanar da zanga-zanga a cigaba da nuna adawa da salon mulkin shugaba Jair Bolsonaro har da matsin lamba da ya yi marabus daga madafan iko.

Rahotanni sun ce zanga-zangar ta fi kamari ne a biranen Rio de Janeiro da Sao Paulo da Brasilia, inda taken "Bolsonaro ya sauka" suka mamaye alluan da ke dauke ga masu boren da ke samun goyon bayan wasu jam'iyyun siyasa.

Ko baya ga batun tsadar rayuwa da ke wani sabon batu da ya kutso a bakunan masu boren, rashin tafiyar da tsari na gari wajen yaki da Corona na zaman babban gimshikin da masu adawa da Bolsonaro ke amfani da shi wajen kalubalantar sa.

A kasa ga shekara daya a gabanin babban zabe a Brazil, wani binciken jan ra'ayin jama'a a watan jiya ya yi nuni da cewa tagomashin Shugaba Bolsonaro na kasa sosai kusa da abokin hamayyarsa Luiz Inacio Lula da Silva na jam'iyyar PT.