Ghana: Zanga-zangar #FixTheCountry
August 4, 2021Zanga-zangar da suka yi wa taken: "#FixTheCountry" ta samo asali ne tun daga shekarar da ta gabata ta 2021, inda hukumomin tsaron kasar ta Ghana suka hana gudanar da ita. Masu zanga-zangar dai, na rajin ganin gwamnatin kasar ta shawo kan matsalar tattalin arziki da tabarbarewar al'amuran tsaro da kuma rashin cika alkawurra daga 'yan siyasa, al'amarin da suka ce yana jefa rayuwar talaka cikin kunci.
Cincirindon wadanda suka halarci zanga-zangar sun hadar da matasa da ma'aikata da magidanta da 'yan kasuwa har ma da matsafa da duk masu ruwa da tsaki a kasar ta Ghana, dauke da allunan rubuce-rubuce kamar rashawa na haifar da talauci, tsadar man fetur ya ishe mu, ku daina tauye 'yancin 'yan jarida. Wasu dai na alakanta wannan zanga-zanga ta lumana da siyasa, Sai dai babbar tambayar ita ce ina ne magaryar tukewar wannan tura idan ta kai bango?