Zanga-zangar ranar ma'aikata
May 1, 2014Masu boren suna adawa ne da shirin gwamnati na gina kasuwar zamani a birnin, inda suka nemi kutsawa wajen dandalin shakatawa da aka sani da Taksim, wanda gwamnatin ke son turewa domin gina sabuwar kasuwa. A bara ma dai dubban jama'a ne suka yi kwanaki suna boren adawa da shirin gwamnati na sare bishiyoy a wajen shakatawan, domin yin sabbin gine-gine. 'Yan sanda sun yi ta cillawa wadanda ke zanga-zangar hayaki mai sa kolla, yayinda su kuwa masu zanga-zangar ke amfani da duwatsu da wasu tarkashen, domin jifan 'yan sandan. Tun da farko dai 'yan sanda sun tushe hanyoyin birnin da dama, inda suke yi wa duk wata hanya da ke zuwa dandalin da aka sani da Taksim gawanya. Koda baki masu bude ido an haramta musu shigewa. Gwamnatin Firaminista Raccip Erdogan na daukar masu boren a matsayin 'yan ta'adda.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu