Zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaba Mursi na Masar | Labarai | DW | 15.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaba Mursi na Masar

Magoya bayan shugaba Mohammed Mursi na Masar sun fito sun yi Allah wadai da tashe-tashen hankulan da suka zargi 'yan adawa da haddasawa

Ɗaruruwan magoya bayan shugaba Mohammed Mursi na Masar suka gudanar da jerin gwano kan tituna ran juma'a domin su yi Allah wadai da tashe-tashen hankulan da aka ɗauki makonni ana yi tsakanin 'yan sanda da masu adawa da gwamnatin Mursi.

Jamiyyar da ta jagoranci jerin gwanon mai taken "Haɗin kan yaƙi da tashe-tashen hankula" ta ɗora alhakin duk rigingimun da suka wakana a 'yan kwanakin baya-bayan nan, kan 'yan adawan da ke ƙarƙashin jagorancin masu ra'ayin sassauci.

Kamfanin dillancin labarun Jamus ya rawaito cewa masu zanga-zangar sun yi ta raira ƙasidu masu yabawa shugaba Mursi yayin da suka yi marci zuwa jami'ar Alƙahira.

Ƙasar Masar dai ya rabu gida biyu tsakanin magoya bayan masu kaifin kishin addini da kuma waɗanda ba ruwansu da addini waɗanda ke neman ganin an raba harkokin gwamnati da na addini.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal