1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi bore a harabar majalisar Ukraine

Abdul-raheem Hassan
June 19, 2018

'Yan sanda sun tarwatsa dubban masu zanga-zanga da suka balle shinge da nufin tsallakawa cikin majalisar dokokin kasar da ke birnin Kiev domin neman ingantuwar rayuwa.

https://p.dw.com/p/2zrH8
Ukraine Kiev - Polizei nimmt Nationalisten beim Versuch fest Gay Parade zu stoppen
Hoto: Imago/Zuma Press/S. Glovny

Masu boren sun hada da tsoffin masu hakar ma'adinai da wadanda suka taimaka wa kasar a yakin Afghanistan a zamanin rusashen Hadeddiyar Daular Soviet a shekaru 33 da suka gabata, inda suke neman gwamnati ta kyautata rayuwarsu da karin alawus.

A yanzu dai an jibge karin 'yan sanda 500 a harabar majalisar, yayin da mataimakin kakakin majalisar Iryna Gerashchenko ya bukaci ganawa da wakilan dukkannin bangarorin da ke boren.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun hatsaniya tsakanin 'yan sanda da tsofoffin mazan jiya a harabar majalisar Ukraine ba, inda ko a watan Maris sai da rikicin ya barke sannan wani rikin ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu a shekarar 2015.