Zanga-zangar matuka Tasi a Faransa | Labarai | DW | 26.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar matuka Tasi a Faransa

A filin tashi da saukar jiragen sama na Orly, daya daga cikin masu zanga-zangar ya samu rauni bayan da wata motar bus ta kutsa kai duk da shinge da aka sanya.

An shiga yanayi na fargaba bayan da direbobin Tasi suka rufe hanyoyi bayan da suka sanya wa tayoyi wuta a wannan rana da suka kira" bakar Talata" wacce ke zuwa a daidai lokacin da masu aikin kula da tashi da saukar jiragen sama suka shiga yajin aiki, haka ma'aikatan gwamnati da na lafiya da malaman makaranta.

A filin tashi da saukar jiragen sama na Orly daya daga cikin masu zanga-zangar ya samu rauni bayan da wata motar bus ta kutsa kai duk da shinge da aka sanya sai dai 'yan sanda sun bayyana cewa an kama direban bus din.

Kimanin masu tuka tasin 300 ne suka tada bore bayan da ake samun masu motoci na kansu da basu da lasisi na haya na musu kutse a aikinsu abin da suka ce na nakasu ga hanyarsu ta cin abinci a cewar Ibrahima Sylla mai magana da yawun kungiyar matukan motocin hayar na Faransa.

An dai samu rahotanni da ke cewa an soke jirgi daya daga cikin biyar da ke tashi daga Orley ko Paris bayan da masu aikin kula da tashi da saukar jiragen suka shiga yajin aiki saboda neman a biya musu wasu bukatunsu.