Zanga-zangar mata a Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 27.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar mata a Jamhuriyar Nijar

Mata sun nuna rashin jin dadin samun mukaman da suka dace cikin sabuwar gwamnatin Jamhuriyar.

Mata sun yi zanga-zanga domin nuna rashin amincewa kan rashin samun mukamai masu yawa kamar yadda kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar ya tanada. Matan sun ce gwamnati tana biris da bukatun da suka gabatar. Matan sun yi dafifi a ofishin kula da mata da ke birnin Yamai fadar gwamnatin kasar.

 

Kungiyoyin mata da suka jagoranci zanga-zangar sun ce gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta nuna wariya ga mata a rabon manyan makamai na ministoci a kasar. Saboda rashin samu kashi 25 cikin 100 da dokar kasa ta tanada ga mata. Matan sun yi korafin cewar kashi 18 cikin 100 suka samu a sabon mukamun na ministoci, inda suka tashi da ministoci takwas daga cikin 42 da majalisar ministocin ta kunsa. Matan sun dade suna kokawa da gwamnatin shugaba Mahamadou Issoufou kan rashin samun mukamai masu yawa.

Sauti da bidiyo akan labarin