'Yan sanda sun hana zanga-zanga a Faransa
June 22, 2016Talla
Kungiyoyin kwadagon dai sun shirya wannan zanga-znagar ne, domin nuna bacin ransu kan batun dokokin aki da mahukuntan kasar ke son yi wa kwaskwarima. Da ma dai gwamnatin kasar ta yi barazanar daukar matakan da suka dace tun bayan da wata zanga-zanga ta rikide zuwa tashin hankali a birnin Paris na kasar ta Faransa a makon da ya gabata. Ko da yake gwamnatin ta ce za ta iya basu damar yin zanga-zangar a wasu lokutan a birnin na Paris, sai dai tuni kungiyar kwadagon kasar ta sa kafa ta yi fatali da wannan tsari, tare da yunkurin fitowa a dukka titunan birnin domin gudanar da zanga-zangar.