Zanga-zangar kin jinin gwamnati a Iraki | Labarai | DW | 15.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar kin jinin gwamnati a Iraki

'Yan Iraki na neman gwamnati ta sauya kamun ludayinta game da matsalar cin hanci da rashawa da ke ci musu tuwo a kwarya tare da gudanar da ayyukan raya kasa..

Dubban 'yan Iraki sun gudanar da zanga-zanga a Bagadaza babban birnin kasar da nufin tilasta wa gwamnati daukan matakan yaki da dabi'ar nuna son kai da kuma cin hanci da karbar rashawa. Babban limaman Shi'an nan Moqtada Sadr ne ya yi kira ga magoya bayansa da su tayar da kayar baya, domin a samu sauyin gwamnati tare da aiwatar da alkuwuran da Firaminista Haider al-Abadi ya yi wa 'yan Iraki.

Su dai masu zanga-zanga sun yi buris da gargadin da rundunar soje da kuma gwamnatin Iraki suka yi musu, na soke gangamin da suka shirya saboda ya na barazana ga yakin da suke yi da 'yan ta'adda.

Cikin wata sanarwar da ya fitar Moqtada Sadr ya bukaci gwamnati da ta sauke duk manyan jami'anta da ake zargi da sama da fadi da dukiyar kasa daga mukamansu tare da gurfanar da su gaban kuliya. Sannan kuma ya nemi da a kafa gwamnati da zata kunshi kwararru zalla maimakon 'yan siyasa.