Zanga-zangar dalibai a kasar Turkiya | Labarai | DW | 19.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar dalibai a kasar Turkiya

Dalibai sun tayar da kayar don nuna adawa da shirin sare bishoyoyi domin samar da hanya a birnin Santambul. Sai dai 'yan sanda sun tarwatsasu da hayaki mai sa hawaye.

'Yan sandan kasar Turkiya sun tarwatsa dalibai da ke zanga-zanga kan fara aikin hanya da ta wuce zuwa jami'arsu da ke Ankara babban birnin kasar, a dai dai lokacin da ma'aikata suka fara sare bishiyoyin dake filin shakatawa na Jami'ar fasaha da ake yi wa lakabi da ta yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun bayyana cewa dalibai da dama ne suka mamaye kofar shigan filin shakatawar suna masu nuna adawarsu da sare kimanin bishiyoyi dubu uku da mahukuntan kasar suka shirya yi domin yin aikin hanyar. An dai kwashe tsahon makwanni ana tataburza a kan wanna aiki.

'Yan sanda sun yi amfani da harsasan roba da hayaki mai sa hawaye domin murkushe daliban dake zanga-zangar nuna kin amincewa da sare bishiyoyin, a filin shakatawar da ya kasance daya daga cikin filayen da suka fi yawan bishiyu a kasar, tun daga farkon watan Satumbar da ya gabata.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe