Zanga-zangar adawa da tazarce a Burundi | Labarai | DW | 27.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar adawa da tazarce a Burundi

Ana ci gaba da dauki ba dadi a kasar Burundi tsakanin matasa masu zanga-zangar adawa da tazarce da jami'an kwantar da tarzoma da ke kokarin tarwatsa su.

Zanga-zangar adawa da tazarce a Burundi

Zanga-zangar adawa da tazarce a Burundi

Rahotanni sun nunar da cewa jami'an kwantar da tarzoma sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kulake yayin da suka fesa ruwan zafi a kan masu zanga-zangar domin tarwatsa su. Masu zanga-zangar wadanda yawancinsu matasa ne da ke adawa da shirin shugaban kasa Pierre Nkurunziza na yin tazarce sun sha alwashin ci gaba da fitowa kan tituna har sai bukatarsu ta biya, kamar yanda wani matashi ke cewa ba zai daina fitowa kan titi domin yin zanga-zangar ba har sai Shugaba Nkruziza ya dakatar da shirinsa na yin tazarce. 'Yan adawar kasar ta Burundi dai na zargin shugaba Nkurunziza da karya yarjejeniyar Arusha wacce ta tanadi wa'adi biyu ga shugaban kasa, inda ya ke neman sake tsayawa takara a karo na uku.