Zanga-zangar adawa da shugabar Brazil | Labarai | DW | 15.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar adawa da shugabar Brazil

Dubban mutane a Brasil sun yi zanga-zangar nuna rashin gamsuwarsu da koma-bayan tattalin arziki da zargin cin hanci da ake wa gwamnatin shugabar kasar Dilma Rousseff.

Brasilien Antiregierungsproteste in Rio de Janeiro

Dubban masu zanga-zanga a Brasil dauke da tutocin kasar

Zanga-zangar dai ta wakana ne a kusan dukkan manyan biranen kasar, inda mutane kimanin dubu ashirin suka halarci gangamin da aka yi a babban birnin kasar Brasilia, yayin da wasu dubu sha biyar suka yi tasu zanga-zangar a birnin Rio de Janeiro.

Masu aiko da rahotanni suka ce masu zanga-zangar sun yi ta rera kalami na kin jinin gwamnatin Ms. Rousseff, inda suka bukaci a tsige ta daga kan mulki yayin da wasu ke kiran soji su yi juyin mulki don kawo karshen jagorancin da jam'iyyar Workers Party ta shefe shekaru sha biyu ta na yi.

Manyan 'yan siyasa na Brazil din ciki kuwa har da na hannun daman Ms. Rousseff ne suke fuskantar bincike kan badakala ta biliyoyin daloli da aka yi a kamfanin mai na kasar wato Petrobras.