Zanga-zangar adawa da Mugabe | Labarai | DW | 26.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar adawa da Mugabe

'Yan sanda sun tarwatsa gangamin masu adawa da mulkin Robert Mugabe na kasar Zimbabuwe.

'Yan sandan Zimbabuwe sun harba hayaki mai sa hawaye a kan shugabannin 'yan adawar kasar Morgan Tsvangirai da tsohon mataimakin shugaban kasar Joice Mujuru yayin da gangamin zanga-zangar adawa da shugaban kasar Robert Mugabe ta rikide zuwa tarzoma.

Tuni Morgan Tsvangirai da Mujuru suka fice daga wurin taron gangamin a motocin su a cewar wadanda suka shaidar da lamarin. A 'yan watannin baya bayan nan dai jami'an tsaron sun zafafa dirar mikiya sakamakon karuwar zanga-zangar adawa da shugaba Mugabe da Jam'iyyarsa ta ZANU-PF yayin da jama'a suke nuna bacin rai kan tabarbarewar tattalin arziki da rashin ayyukan yi da kasar ke fama da su.