Zanga-zangar adawa a Kenya | Siyasa | DW | 07.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar adawa a Kenya

'Yan adawa a Kenya sun ce lallai sai gwamnati ta biya mu su bukatunsu, ko su ci gaba da zanga-zanga

Dubban alummar kasar Kenya a ranar Litinin dinnan sun gudanar da wata gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnati a babban dandalin taron birnin Nairobi. Babban dalilin da ya sa yan adawa shirya wannan zanga-zanga shine ganin yadda gwamnati taki amincewa da komawa teburun tattaunawa da bangaren nasu sai suka bukaci amfani da wannan dama wajen bayyanawa alummar kasar bukatunsu a wurin gwamnati.

Jagoran adawa kuma tsohon Firaminista Raila Odinga ya shirya wannan zanga-zanga da zummar cewa zai bayyana manya-manyan bangarori da gwamnatin ta tafka kura-kurai ciki kuwa harda ci gaban tabarbarewar tsaro. Alfred kiti shine wakilin DW a wajen wannan zanga-zanga a Nairobi fadar gwamantin kasar ta Kenya .

Bakatun 'yan adawa ga gwamnatin Kenya

Sun zayyano batutuwa da dama da suka hadar da tsaron da janye dakarun kasar Kenya daga Somaliya da ci gaban cin hanci da rashawa da tsadar rayuwa da danniya da bada fifiko ga wata kabila wajen raba madafun iko, wadannan suke so gwamnati ta yi wani abu akai ko kuwa su dauki mataki.

Tuni dai gwamnatin kasar ta yi zargin cewa kananan jamiyyun siyasa nada masaniya kan harin da aka kai a yankunan dake gabar teku a karshen makon da ya gabata, kuma taron da suka shirya nada masaniya kan irin wannan hari, sai dai suma yan adawar sun maida wa gwamnatin da martani kamar yadda anan ma Alfred Kiti ke cewa.

Sun nisanta kansu daga dukkan abubuwan da ke faruwa, inda sukace wannan matsalace ta ci gaban tabarbarewar tsaro da ke wakana a kasar, kuma hakkine da ya rataya a wuyan gwamnati ta ba wa alummarta tsaro a dukkanin fadin kasar.

Kokarin jami'an tsaro

Jamian tsaro dai sun yi yunkurin hana wannan zanga-zanga inda suka harba hayaki mai sa hawaye cikin kokarin gwamnati na dakile yunkurinnasu, sai dai kundin tsarin mulkin kasar ya bawa alumma damar neman hakkinsu ta hanyoyi da dama ciki kuwa harda yin irin wannan gangami kamar yadda wakilin na DW Alfred kiti ke cewa.

daftarin tsarin mulkin kasa ya bawa alumma damar yin zanga-zanga da zata iya kaiwama ga tube shugaban kasa, idan har mahukuntan suka gaza biya musu wadannan bukatunasu dole alummar kasar ta Kenya su ci gaba da daukar mataki na adawa da gwamnati.

A cewar bangaren gwamnati dukkanin wadannan bukatu da yan adawar suka gabatar, sune abubuwan da ta dukufa tana aiki a kansu dan haka bata ga dalilin wannan gangamiba.

Zaman zulumi dai na ci gaba da karuwa a wannan kasa ga kuma zargin da mahukunta kewa kafafan yada labarai na kokarin iza wutar rikici harda bada gargadin cewa ya saba wa doka wani ya yi amfani da yanar gizo wajen watsa wasu labarai da zasu iya harzuka alumma da kyamar gwamnati.

Sauti da bidiyo akan labarin