Zanga-zanga kan farashin burodi a Sudan | Labarai | DW | 07.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga kan farashin burodi a Sudan

Masu zanga-zanga sun fantsama kan tituna a kasar Sudan saboda nuna takaici da tashin farashin burodi a kasar inda daga bisani suka yi artabu da 'yan sanda.

'Yan sandan kasar ta Sudan sun yi amfani da hayaki mai saka hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga da suka toshe tituna a birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar gami da wasu sassa na kasar wadanda suke nuna takaici bisa tashin farashin na burodi.

'Yan sandan har wa yau sun yi artabu da daliban jami'ar birnin Khartoum, sannan an samu makamanciyar wannan zanga-zanga a Lardin Darfur da wasu sassa na kasar. Gwamnati ta bayyana shawo kan lamari. Yanzu haka gwamnatin dai na neman hanyar dakile zanga-zangar domin kar a sake shiga makamancin tashin hankali da aka samu a shekara ta 2013 da mutane da dama suka hallaka lokacin da gwamnatin kasar ta zabtare tallafi da aka saba badawa.