1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Girka saboda shirin tsuke bakin aljihu

Abdourahamane HassaneMay 8, 2016

Sama da mutane dubu 15 suka yi gangami a cikin wasu biranen na Girka domin yin Allah wadai da shirin gwamnatin Alexis Tsipras na tsuke bakin aljihu.

https://p.dw.com/p/1Ijxp
Griechenland Generalstreik Demo in Athen
Hoto: Reuters/A. Konstantinidis

Shirin ya tanadi ƙara kuɗaɗen haraji da zabtare kuɗaɗen fansho da kuma korar wasu dubban ma'aikatan daga bakin aiki. Ana sa rai majalisar dokokin ƙasar za ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da wani daftarin ƙudirin a yau Lahadi a kan shirin, duk kuwa da matsin lambar da ƙungiyoyin ƙwadagon ke yi wa gwamnatin.

Hukumomin ba da lamuni na duniya su ne suka tilasta wa Girka yin wadannan sauye-sauye gabanin samun ƙarin rance domin tada komaɗar tattalin arzikinta.