ZANGA ZANGA A GARIN BOUAKE;IVORY COAST. | Siyasa | DW | 12.10.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZANGA ZANGA A GARIN BOUAKE;IVORY COAST.

Har yanzu dai tsugune bata kare ba dangane da rikicin yan tawaye a kasar Cotedivoire,duk da yunkurin da MDD keyi na ganin cewa ta kwance damarar yakin yan tawayen kasar da aka dauki shekaru biyu ana fama da rikicinsu.

Kasar ta Cotedivoire dai na cigaba da kasancewa cikin rayuwa na dardar daga bangaren alumma,inda a jiya ma sai da Sojojin kiyaye zaman lafiya sukayi ta fesa barkonon tsohuwa,domin tarwatsa masu zanga zanga a garin Bouake dake hannun yan tawayen.Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana cewa mutane uku ne suka jikkata sakamakon harbin bindiga daga jamian tsaro dake kokarin shawo kann rigimar,ayayinda Dakarun Faransa sukace jamian su 6 ne suka samu raunukan jifan duwatsu daga masu zanga zangar.

Sanarwar Sojojin kiyaye zaman lafiyan MDD na nuni dacewa ,sunyi harbi a iska ne saboda irin barazanar da masu tawayen sukayi.

Rahotanni daga kasar dai na nuni dacewa masu tawayen na gudun abunda zai biyo bayan cikan waadin da dakarun kiyay

 • Kwanan wata 12.10.2004
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvfe
 • Kwanan wata 12.10.2004
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvfe