1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanaga kan 'yan matan Chibok

Usman ShehuMay 8, 2014

Gangamin neman a yi hobbasa wajen ceto 'yan matan da aka sace a Najeriya sai karuwa ya ke yi, musamman a kasashen Yamma

https://p.dw.com/p/1Bwes
Demonstration Freilassung Boko Haram Entführung Schülerinnen Nigeria
Hoto: DW/H. Fischer

►Kasashen Duniya da dama na Allah wadai da sace 'yan matan Chibok fiye da 200 da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi, wanda ya sanya wasu daga cikin kasashen suka tashi suka tsaya wajan tabbatar da an ceto yan-matan. Baya ga dai-dai kun kasashen da suka yi alkawarin taimakawa Najeriya da kwararrun jami'ai, a gefe guda zanga-zangar nuna bacin rai da sace 'yan matan sai karuwa ta ke yi. Wasu 'yan Najeriya da ke zama a birnin Bonn da ke kasar Jamus sun godanar da tasu zanga-zangar, inda suka samu hallartan wasu 'yan kasashen waje.

Al-amarin dai ya sanya 'yan Najeriya da ke zama a nan birnin na Bonn yin zanga-zanga a safiyar yau Alhamis, domin nuna rashin goyon bayansu da faruwar al-amarin da kuma jan hankalin gwamnatin kasar ta Najeriya, don tabbatar da ta ceto 'yan-matan. Kamar yadda Benedict Chijoke daya daga cikin masu zanga-zangan yake cewa"

Demonstration Freilassung Boko Haram Entführung Schülerinnen Nigeria
Hoto: DW/H. Fischer

"Muna zanga-zanga ne domin mu nuna damuwar mu dangane da kannen mu da yan kungiyar Boko Haram suka sace, al-amarin gaskiya bai yi mana dadi ba. Shi ya sa muka hallara domin kalubalantar hallayar yan Boko Haram, kamar yadda 'yan uwanmu da dama suka yi".

Wasu daga cikin wadan da suka yi zanga-zanagar a nan Jamus, sun yi maraba da jin cewa kasashen kamarsu Amirka, Faransa, China da kuma Birtaniya, sun yi alkawarin taimakawa Najeriya wajen yakan yan kungiyar Boko Haram. Adora daya ce daga yan Najeriya da suka yi farin icki da ce ta ce abin farinciki ne da kasar Amurka tace zata taimaka wajan yakan yan Boko Haram

Mawallafiya: Zainab Babbaji

Edita: Usman Shehu Usman