Zamfara: An karfafa matakan tsaro bayan sace dalibai | Siyasa | DW | 04.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zamfara: An karfafa matakan tsaro bayan sace dalibai

A sakamakon yawaitar aiyukan 'yan bindiga ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da aikin hakar ma'adinai dama shawagin jiragen sama a sararin samaniyar jihar Zamfara da ke arewacin kasar.

A ci gaba da kokarin neman mafitar rashin tsaron da ke dada kamari a cikin tarrayar Najeriya, majalisar tsaron kasar ta dakatar da aiyukan hakar ma'adinai a jihar Zamfara, ko bayan haramta shawagi na jirage a cikin yankin. Tun bayan satar mata 'yan makarantar Sakandaren Jangebe da ke cikin jihar ta Zamfara, hankulan daukacin kasar ya karkata ya zuwa sabuwar sana'ar satar dalibai da ke dada samun farin jini a tsakanin 'yan ina da kisan.

DW.COM