Zambiya ta samu sabon shugaba | Labarai | DW | 29.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zambiya ta samu sabon shugaba

An bayyana Guy Scott a matsayin shugaban Zambiya na wucin gadi, bayan mutuwar Shugaban Michael Sata

An fara samun kokuwar neman samun madafun ikon kasar Zambiya bayan mutuwar Shugaba Michael Sata a wannan Talata da ta gabata a wani asibiti da ke birnin London na kasar Birtaniya. Bayan tattaunawa wani ministan gwamnati ya tabbatar da cewa mataimakin Shugaban kasa Guy Scott ya zama shugaba a kasar mai mutane fiye da milyan 15, kuma Bature daya da ke mulki wata kasa a Afirka.

Lokacin da Sata zai tafi jinya ya nada ministan tsaro da shari'a Edgar Lungu a matsayin shugaban wucin gadi. Amma yanzu bisa kundin tsarin mulkin kasar tilas mataimakin shugabar kasa Guy Scott zai zama shugaba kasar har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben cike gurbin mukamun a kwanaki 90 masu zuwa.

Marigayi Michael Sata dan shekaru 77 da haihuwa, ya mulki kasar ta Zambiya da ke yankin kudancin Afirka na tsawon shekaru uku, bayan lashe zaben shekara ta 2011.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu