Zafin rana ya kashe daruruwan mutane a Pakistan | Labarai | DW | 25.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zafin rana ya kashe daruruwan mutane a Pakistan

Matsalar wace ta fi kamari a birnin Karashi ta fi shafar marasa galihu da mabarata da kuma masu aikin karfi a cikin rana.

A kasar Pakistan mutane sama da dubu ne suka mutu a 'yan kwanakin bayannan a sakamakon tsananin zafin rana wanda a karshen makon da ya gabata ya kai murabbadi 45 a ma'aunin zafin rana na Celcius a birnin Karashi birnin mafi girma a kasar da ke kunshe da mutane kimanin miliyon 20. Hukumomin manyan gidajan assibiti sun ce lamarin ya fi shafar marasa galihu da mabarata da kuma masu aikin karfi na cikin rana.

Sai dai hukumomin kasar sun ce suna da fargabar yiwuwar adadin mutanan da za su mutu ya kai dubu da 500 domin akwai da dama wadanda suka mutu a cikin gidajansu ko a gidajan assibiti masu zaman kansu wadanda ba sa cikin lissafi ba kawo yanzu.Wannan matsala ta zo ne a daidai lokacin da al'ummar Musulmin kasar ke gudanar da azumin watan ramadana a yayin da a share daya ake fuskantar matsalar daukewar wutan lantarki a kasar.