Zabukan Amirka, Democrats ta sha kaye | Siyasa | DW | 05.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zabukan Amirka, Democrats ta sha kaye

Jamiyyar adawa ta Republican ce dai ta samu rinjaye a majalisar dattawan Amurka karon farko cikin shekaru takwas, yayin zaben tsakiyar wa'adin mulkin Shugaba Obama.

Kamar yadda sakamakon zaben tsakiyar wa'adin mulkin shugaba Barack Obaman ya nunar, jamiyyar Republican ta samu nasarar lashe kujeru 52 a majalisar dattawan kasar, bayan da Joni Ernst daga lowa ta lallasa Bruce Braley na bangaren jamiyyar Democrat, hakan kuwa ya sanya jamiyyar ta Republican ta samu kujeru bakwai daga wannan yankin.

Samun nasara da yin aiki tare

A cewar Sanata Mitch McConnell mai shekaru 72 a duniya wanda kuma ake sa ran zai zamo shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Amirkan masu kada kuri'a sun kagu da ganin samun sabon shugabanci. Haka kuma ya ce dole su yi aiki da bangaren adawa domin ciyar da Amirka gaba.

Farincikin sanatna daga jam'iyyar adawa ta Republican Mitch McConnell.

Farincikin sanatna daga jam'iyyar adawa ta Republican Mitch McConnell.

"Muna da alhaki da ya rataya a wuyanmu dole muyi aiki tare inda za mu hadu mu amince. A tunanina wannan shi ne aikinmu, dan kawai muna da tsarin jam'iyyun siyasa biyu ba ya nufin za mu yi ta zama muna kalubalantar junanmu”.

Ita ma abokiyar takarar McConnell daga jamiyyar Democrats da ta sha kaye a zaben na majalisar dattawa Alison Lundergan Grimes, ta ce za su ci gaba da fafutuka wajen ganin biyan bukatun al'ummar jiharsu ta Kentucky.

"Duk da cewa ba mu samu nasarar da muka tsammaci samu ba a wannan tafiya, zan ci gaba da kokarin kwato hakkokin al'ummar Kentucky a ko da yaushe a kuma kowace rana, fatana shi ne na gabatar da sako ga al'ummarmu cewa akwai bukatar mu yi aiki tare wajen ganin an inganta mafi karancin albashi, a rufe gibin da ke akwai wajen biyan mabanbantan jinsi, sannan a samar da ayyuka da zasu rika samawa mutane albashi mai kyau ga daukacin al'ummar Kentucky".

Jam'iyar Republican na murnar samun nasara.

Jam'iyar Republican na murnar samun nasara.

Kalubale ga Shugaba Obama

Wannan sabuwar nasara dai da jamiyyar ta Republican ta samu shine rinjaye mafi girma da ta samu tun bayan yakin duniya na biyu, inda yanzu jamIyyar ke da kujeru 52 sabanin 45 din da ta ke da shi a baya a majalisar dattawan da ke da kujeru 100, kuma hakan na zaman babban kalubale da ke gaban shugaba Obama da yanzu zai jagoranci kasar cikin shekaru biyun da suka rage masa a wa'adin mulkinsa na biyu, kasancewar jam'iyyar adawa ce ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar a yanzu.

Sauti da bidiyo akan labarin