Zaben shugaban kasa karo na 12 a Iran | Labarai | DW | 19.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa karo na 12 a Iran

Tun bayan juyin juya halin da aka yi a shekarar 1979 kimanin shekaru 40 da suka gabata, a wannan Jumma'a ce ake gudanar da zaben shugaban kasa da gwamnoni karo na 12 a Iran.

Iran wahlen 2017 (Irna)

Ayatullah Ali Khamenei jagoran Muslunci na kasar Iran

Al'ummar kasar Iran na kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar da ke gudana, inda shugaba mai ci Hassan Rohani ke fafatawa da dan takara mai ra'ayin rikau Ebrahim Raissi. Jagoran Muslunci na kasar Ayatullah Ali Khamenei bayan ya yi zabe, ya yi kira ga 'yan kasar ta su fita su yi na su zaben da wuri:

"Idan mutun zai gudanar da wani abu mai muhimmanci irin wannan, to ya kyautu ya yi shi tun da wuri, domin makomar kasar Iran na a hannun 'yan kasarta da za su zabi wanda zai kasace shugaban zartaswa."

Akalla dai 'yan kasar ta Iran miliyan 56 da dubu hudu ne za su zabi shugabansu tsakanin 'yan takara hudu cikinsu kuwa manyan 'yan takara biyu, inda zaben ke kasancewa na tsakanin ci gaba da akidar da Rohani ya somo ta buda kofofin kasar ga sauran kasashen duniya, da kuma bin tsarin ra'ayin rikau da dan takara Raissi ya sa wa gaba.