Zaben shugaban kasa cikin matsi a Ghana | Labarai | DW | 07.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa cikin matsi a Ghana

Zaben kasar na fiskantar barazana kasancewar ana da shakku kan zaman hukumar zaben kasar a matsayin mai 'yancin gashin kanta.

A ranar Laraban nan al'ummar kasar Ghana na zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa, zaben da ke zama zakaran gwajin dafi ga cigaban daidaituwar dimokradiya a wannan kasa da ke fama da rikici a fannin tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa.

Kasar da ke zama wacce Shugaba Barack Obama na Amirka ya kwarzanta da zama abar koyi a fannin zaman lafiya da mika mulki cikin kwanciyar hankali, yanzu zaben kasar na fiskantar barazana kasancewar ana da shakku kan zaman hukumar zaben kasar a matsayin mai 'yancin gashin kanta.

Shugaban kasar John Mahama na neman a sake zabensa inda ya ke fafatawa da Nana Akufo-Addo, fitaccen dan siyasa da ke amfani da halin da kasar ke ciki da ma batun badakalar cin hancin wajen tallata hajarsa ta neman shugabancin kasar ta Ghana.

Kimanin mutane miliyan 15 ne dai suka yi rijista a zaben kasar da ke zama mai muhimmanci a Yammacin Afirka da ke fitar da albarkatun koko da zinare da albarkatun mai.