1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a kasar Togo

Zainab Mohammed Abubakar
February 21, 2020

A wannan Asabar din ce al'ummar kasar Togo ke kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa. Masu sa ido kan zaben ba sa zaton wani sauyi duba da yadda iyali guda suka shafe tsawon shekaru suna mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/3Y8CK
Togo Präsidentschaftswahlen
Hoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

'Yan takara da dama ne dai ke zawacin kujerar shugaban kasar kuma za su yi wannan tara ce shugaban kasar Faure Gnassingbe wanda ke kan gadon mulki tun shekarar 2005. Tuni dai babban birnin kasar Lome da ma sauran sassan kasar suka dau harami, inda magoya bayan 'yan takarar suka lika hotunan gwanayensu baya ga gangami da ke cigaba da gudanarwa don neman kuri'un mutane.

Kusan 'yan kasar miliyan hudu ne dai za su kada kuri'unsu a wannan zaben kuma jama'a na ta bayyana fatansu kan abin da suke son ganin sabon shugaban da za a ya yi. Djabara Moustapha wata matashiya ce 'yar shekaru 20 da ke dab da kammala karatunta na jami'a a Lome, ta kuma ce ''ina fatan duk shugaban kasa da za a zaba zai samar wa matasa ayyukan yi''. Togo dai na fama da matsaloli na talauci da rashin kayayyakin more rayuwa da karancin albashi mai kyau ga ma'aikata kamar likitoci. Kashi 59 na al'ummar kasar miliyan 7 da dubu dari tara  yara ne da matasa da shekarunsu ke kasa da 25. A cewar Roger Folikoue farfesa a fannin siyasa da shari'a a jami'ar Lome mahukuntan kasar na amfani da talauci wajen danne jama'a.

Togo Protest #Faure Must Go
'Yan adawa na fatan ganin jam'iyya mai ci ta kau daga gadon mulkiHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei
Togo Wahl Oppositonsführer Jean-Pierre Fabre
Madugun 'yan adawa Jean-Pierre Fabre ya yi alkawarin kawo sauyi in ya lashe zabeHoto: picture-alliance/Ange Obafemi/Panapress/Maxppp

Togon dai ita ce kasa daya tilo a yankin yammacin Afirka da ke karkashin mulkin 'yan gida daya. A shekara ta 1967 mahaifin Gnassinbe, wato Eyadema ya hau mulki bayan kifar da gwamnati. Kafa jam'iyyun siyasa masu yawa da gajeren wa'adin gwamnatin riko na Joseph Kokou Koffigoh a farkon shekarun 1990 ya gaza sauya tsarin siyasar kasar. 

Tun daga zaben shekarata 2015 kawo yanzu dai, zanga-zangar adawa da gwamnatin Togon ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 25, kuma yadda yakin neman zaben na ranar Asabar ke tafiya akwai ban takaici, a cewar Aime Adi daraktan kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International a kasar inda ya ke cewar ''yakin neman zaben a shafukan sada zumunta ya kasance mai sarkakiya. Abun takaici saboda mahawarar ta koma yadda mutane ke tafiyar da rayuwarsu. An manta da manufofin dan takarar wa jama'a. Labarin ya karkata zuwa kan dan da mutum ya haifa da wacece, kuma ina ya taba yin aiki''.