1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar kafofin sada zumunta a zaben Najeriya

Nasir Salisu Zango RGB
February 24, 2019

Kafofin sadarwa na zamani da ake wa lakabi da social media na taka muhimmiyar rawa wajen zabukan kasar, amma ana zargin sun taimaka wajen rura wutar rikici da bayar da labarai irin na kanzon kurege.

https://p.dw.com/p/3Dzxc
Wähler in Nigerias Hauptstadt Abuja
Hoto: DW/Uwaisu A. Idris

A Najeriya, tun a zaben 2015 wanda a karon farko jam'iyyar adawa ta rangada jamiyya mai mulki da kasa aka fara fahimtar tasirin wadannan kafofi, sai dai kuma a ra'ayin Dr Ibrahim Musa kwararren mai yada labarai a irin wadannan kafafe, ya ce duk da tasirin kafofin sada zumunta na zamanin, kafar na kuma kawo nakasu wajen bayar da dama ga masu yada labarai na kanzon kurege wanda kuma a lokuta da dama kan jawo tarzoma.

Sai dai kuma a ra'ayin Jafar Jafar dan jarida kuma mamallakin jaridar nan da ake wallafawa ta dandalin sada zumuntan na zamani wato Daily Nigeria ya ce babu shakka social media na da tasiri sosai wajen fitar da alkaluman sakamakon zabe tare da rage magudi, koda yake ya ce hankaka ce tana da fari da baki.

Kadan daga cikin tasirin kafafen sada zumunta na zamanin shi ne, fitar da alkaluma tun ma kafin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da nata sakamakon a hukumance, domin a yanzu haka ana can ana kirga kuri'un zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a sassan Najeriyar daban-daban, amma kuma tuni sakamakon zaben ya dade yana yawo a kafafen sada zumunta na zamanin. Babu dai yakini kan gaskiyar sakamakon, kasancewar labaran Social Media jita-jita ce idan ka kama ta ka kama karya,  idan kuma ka saki ka saki gaskiya.