1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Zaben Jamus: Yan takara sun tafka muhawara

February 17, 2025

Manyan 'yan takarar kujerar Shugaban Gwamnatin Jamus sun fuskanci sauran kananan 'yan takara tare da tafka muhawarar fuska da fuska ta kafar Talabijin gabanin zaben ranar Lahadi mai zuwa.

https://p.dw.com/p/4qZYo
Yan takarar Shugaban Gwamnatin Jamus Scholz da Habeck da Merz da kuma Weidel
Yan takarar Shugaban Gwamnatin Jamus Scholz da Habeck da Merz da kuma WeidelHoto: Kay Nietfeld/dpa-Pool/picture alliance

Ku san za a iya cewa wannan ne karon farko da magoya bayan 'yan takarar suka gansu a inuwa guda ta kafar talabijin da suka hada da Shugaban Gwamnati mai ci Olaf Scholz na Jam'iyyar SPD da  Friedrich Merz na CDU  da Robert Habeck na The Greens da kuma and Alice Weidel ta jam'iyyar AfD mai ra'ayin kyamar baki.

Karin bayani: Scholz ya soki abokin karawarsa kan hadaka da AfD 

A yayin muharar Mr. Scholz ya jaddada cewa gwamnatinsa ta taka rawar gani wajen takaita shigowar bakin haure cikin Jamus da kashi 17 bisa 100. Ita kuwa Weidel ta jam'iyyar AfD mai ra'ayin kyamar baki ta caccaki jam'iyyun  SPD, CDU da kuma Green kan goyon bayan da suke bai wa Ukraine, inda ta ce kamata ya yi Jamus ta kasance 'yar kallo a yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.


 

Merz na jam'iyyar CDU da ke kan gaba ya ce yana kallon SPD da Greens a matsayin kawancen jam'iyyun da za su kafa gwamnati.