1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben gama-gari ya samu karbuwa a Zimbabuwe

Mouhamadou Awal Balarabe
July 30, 2018

Miliyoyin 'yan Zimbabuwe sun kada kuri'a cikin tsanaki a karon farko bayan faduwar gwamnatin tsohon shugaban kasa Robert Mugabe sai dai zaben gama-garin ya gudana cikin yanayi na zargin magudin zabe daga bangaren adawa.

https://p.dw.com/p/32L8V
Simbawe Präsidentschaftswahlen Wähler
Hoto: Reuters/S. Sibeko

'Yan Zimbabuwe sun fara layi a gaban runfunan zabe tun da  karfe 4 na asuba don tabbatar da cewa sun kada wa dan takararsu kuri'ar da za ta bashi damar lashe zabe. Dukkaninsu sun yi zabe cikin 'yanci da walwala, sabanin shekarun baya inda gwamnatin Shugaba Robert Mugabe ke uwa da makarbiya a harkokin zabe. Akasarin 'yan kasar na fatan wannan zabe ya dora kasar kan tafarkin ci gaba ko ma da wace jam'iyya ce ta samu nasara a cewar wata mace bayan da ta kada kuri'arta a Harare inda ta ce ''nasara za ta iya samuwa a kowane bangare. Muna maraba da duk bangare idan akwai canjin da zai kawowa. "

Bildkombo Simbabwe Präsidentschaftswahlen Mnangagwa Chamisa
Ko waye zai kasance shugaban Zimbabuwe na gaba tsakanin Mnangagwa da Chamisa?Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wannan dai shi ne karon farko da aka samu 'yan takara 23 a zaben shugaban kasa a Zimbubuwe. Sai dai hankalin 'yan kasar ya fi karkata kan shugaban kasa Emmerson Mnangagwa, dan takarar jam'iyyar ZANU-PF da ke ikon tun bayan da Zimbabuwe ta samu 'yancin kai a 1980 da kuma sabon madugun 'yan adawa Nelson Chamisa da ke jagorantar jam'iyyar MDC.

'Yan adawa na korafi dangane da yiwuwar tafka magudin zabe kamar yadda gwamnati ta saba. Sai dai a karon farko cikin 16 da suka gabata, masu sa ido na kasashen ido sun shaidar da yadda zabe ya gudana a Zimbabuwe. Elmar Brok dan siyasa na kasar Jamus da ke jagorantar tawagar masu sa ido na EU ya ce ba zai yi saurin yabo ba matikar ba a tabbatar da sahihancin zaben ba.

Elmar Brok
Elmar Brot ya jagoranci tawagar masu sa ido na EU a zaben ZimbabuweHoto: DW/C. Teixeira

Kididdigar jin ra'ayin jama'a ta nunar da cewa dan takarar Zanu-PF Emmerson Mnangagwa ya fi samun karbuwa tsakanin al'umma. Sai dai kuma za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa idan ba wani dan takara da ya samu fiye da 50 cikin 100 na kuri'in da aka kada. Baya ga zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa, ana kuma gudanar da zaben kananan hukumomi duk a lokaci guda.