Zaben Burundi ya janyo sabuwar zanga-zanga | Siyasa | DW | 21.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben Burundi ya janyo sabuwar zanga-zanga

Matasa da dama suka fara zanga-zangar nuna adawa da zaben bayan da aka tabbatar da mutuwar wani dan sanda da ma wani dan adawa a sakamkon rikicin da ya barke a wasu wuaren jefa kuri'ar

Kasar Burundi ta gudanar da zaben shugaban kasa ranar talata, amma sai dai, zaben ya zo da tangardan rasa rayuka wanda ya jawo zanga-zanga, bayan da wasu ungwannin suka wayi gari da karar harbin bindiga. Wani jami'in dan sanda da ma wani dan jam'iyar adawa na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a rikicin zaben kasar Burundin, wannan ne ma ya haifar da zanga-zangar kyamatar wannan zabe, musamman dan dagewar da shugaba Nkurunziza ya yi na tsayawa takara a wannan zabe.

Sukar lamirin shugaban ne ma dai, da fargaban abinda ka iya biyo baya, ya hana wasu 'yan kasar fita rumfunan zaben dan kada kuri'unsu, kamar yadda Wanan dan Burundi da ke da zama garin Musenyi ya bayyana:

"Na zo nan ne domin in kada kuri'a da nufin zaben sabon shugaban kasa. Ni ma cikakken dan Burundi ne. Sannan kuma na yi zabe ne don ina jin tsoro."

Saurari sauti 03:15

Hira a kan Burundi da Sadiq Abba dan jarida kuma mai sharhi

Shi ma Jean Claude Musenyi, wanda ke da zama a lardin Bubanza da ke yammacin Burundi ya bayyana dalilansa na fita don yin wannan zabe.

" 'Yanci na, na kada kuri'a ne ya kawo ni, kuma nauyi ne ga duk wani dan kasa na zaben wanda ya ke ganin cewar shi ne zai gudanar da ayyuka na gari. Ina fatan cewar Nkurunziza zai lashe zaben saboda mutane da dama na goyon bayan shi. Ya gina asibitoci da dama da kuma makarantu. Sannan kuma ya samar da wuntar lantarki da kuma tsaftacaccen ruwan sha da sauransu."

Nkurunziza ya fita zabe a kan kekenshi

A yayin da jama'a ke ta fargabar abin da iya biyo bayan zaben domin kunen uwan shegun da Nkurunziza ya yi, shi kansa ya je rumfan zaben dan kada kuri'arsa a kan keke, kuma ga karin bayanin da ya yi:

"kamardai yadda kuka sani, Mutane ne zasuyi zaben bisa cancanta. musamman wajen la'alari da aiyukanda aka masu a baya da kuma wanda ake shirin yi musu nan gaba.kuma na tabbata mutane zasui karatun tasunu wajen zaben wanda zai shugabanci kasar dan kawo ci gaba da zai raya Dimokradiya harma a samu zaman lafiya a kasar"

A yanzu dai 'yan Burundin na cikin fargaba ganin yadda matasa suka tada zanga-zanga har da rufe manyan titunan Babban Birnin kasar Bujumbura, musamman bayan da aka tabbatar cewa da gawar jami'in jam'iyar adawa.

Sauti da bidiyo akan labarin