1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamkon farko a zaben Afirka ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 9, 2019

Matsalolin tatalin arziki da ilimi da cin hanci da karbar rashawa na zaman babban kalubale ga shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.

https://p.dw.com/p/3IEzX
Südafrika Parlamentswahl Stimmauszählung
Fara kidayar kuri'u a Afirka ta KuduHoto: Reuters/R. Ward

Sakamakon farko na 'yan majalisun dokoki da na larduna a kasar Afirka ta Kudu, na nuni da cewa jam'iyyar ANC mai mulki ce ke kan gaba da kaso 55 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Wannan dai na zaman zaben gwaji ga Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar, a kokarinsa na farfado da karfi da kuma mutuncin jam'iyyar. Mai shekaru 66 a duniya, Ramaphosa ya dare kan karagar mulkin kasar ne a bara, bayan da jam'iyyar ta ANC ta tilasta tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ya ajiye mukaminsa sakamakon badakalar cin hanci.