1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben 'yan majalisa a Afirka ta Kudu

Mohammad Nasiru Awal GAT
May 7, 2019

A wannan Laraba takwas ga watan Mayu za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu inda hasashe ya nunar da cewa jam'iyyar ANC mai mulki ce za ta lashe shi.

https://p.dw.com/p/3I5Eo
Südafrika Kommunalwahlen
Hoto: picture-alliance/AP Photo


A wannan Laraba wato takwas ga watan Mayu za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu, lamarin da ya kasance babban kalubale a yakin neman zabe na Shugaban Kasa Cyril Ramaphosa da jam'iyyar ANC mai jan ragamar mulkin kasar. Sai dai duk da matsalolin da kasar ke ciki, hasashe na nuna cewa jam'iyyar ta ANC ce za ta lashe zaben. 

Shekaru 25 da karshen mulkin nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, masharhanta sun bayyana hali na koma-bayan siyasa da zamantakewa da tattalin arziki a kasar. Bashin da ke kan gwamnati na zama abin damuwa, yayin da yawan marasa aikin yi ya kai kashi 27 cikin 100, sannan sama da rabin matasan kasar na zaman kashe wando a cewar Melanie Müller ta gidauniyar nazarin kimiya da siyasa da ke birnin Berlin a Jamus, da kuma ke sharhi kan kasar ta Afirka ta Kudu:


 "Akwai jerin matsaloli musamman a bangaren tattalin arziki da ci-gaban kasa. Bugu da kari zaben gaba daya ya ta'allaka ne da abubuwan da suka faru lokacin shugabancin Zuma, wanda aka maye gurbinsa a watan Fabrairun bara."

Südafrika Wahlkampf ANC Cyril Ramaphosa
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu Hoto: Getty Images/AFP/R. Jantilal

Masharhanta da dama na dora wa jam'iyyar ANC wadda tun a 1994 take kan ragamar mulki, wani kaso na matsalolin da Afirka ta Kudu ke fama da su. Ana zargin da yawa daga cikin 'ya'yanta musamman tsohon Shugaba Jacob Zuma wanda ya yi mulki daga 2009 zuwa 2018 da hannu na tabarbarewar tattalin arziki da cin hanci da rashawa da suka yi wa kasar katutu, musamman dangane da dangantakarsa da iyalin Gupta. Cyril Ramaphosa da ya gaji Zuma ya alkawarta bude sabon babi na canje-canje da farfado da tattalin arzikin kasa tare da daukar matakan ba-sani ba-sabo a yaki da cin hanci. Sai dai masana irinsu Melanie Müller ta gidauniya nazarin kimiya da siyasa Berlin na ganin da jan aiki a gaba:


 "Babbar tambaya a nan ita ce ko matakan da Ramaphosa ya dauka kawo yanzu sun isa sun maido da yarda cikin jam'iyyar? A ganina akwai mutane da dama a Afirka ta Kudu da ke fatan a dauki tsauraran matakai a kan wadanda aka samu da laifi ciki har da ministoci. Sai dai har yanzu akwai mukarraban Zuma a cikin majalisar ministocin kasar, wanda hakan bai yi wa masu zabe dadi ba."

A yakin neman zabe jam'iyyun adawa kamar Democratic Alliance wato DA na amfani da wannan damar suna masu alkawarta gina sabuwar kasa ta Afirka ta Kudu wadda babu gurni na cin hanci da rashawa a cikinta a cewar shugabanta Mmusi Maimane da ke zama bakar fata na farko da ya jagorancin jam'iyyar ta DA da a zaben 2014 ta samu kujeru 89 abin da ya ba ta matsayi na biyu a majalisar dokoki. Wadda ka biye da ita a matsayi na uku, ita ce jam'iyyar Economic Freedom Figters wato EFF karkashin jagorancin tsohon dan ANC, Julius Malema. Jam'iyyar ta yi suna wajen neman kwace manyan filaye daga hannun daidaikun mutane.

Südafrika Misstrauensvotum gegen Präsident Zuma
Majalisar dokokin Afirka ta KuduHoto: picture alliance/dpa/AP/Pool/R. Bosch

Wani batu da ya dauki hankali a yakin neman zabe shi ne yawan kai wa baki hari a kasar. Antonio Capalandana dan jarida ne da ya shafe shekaru 10 yana zaman ci-rani a Afirka ta Kudu da ya ce a kullum baki na cikin zaman fargaba a kasar:

 "Gibi tsakanin matalauta da masu arziki ya yi yawa a lokacin wannan gwamnati ta ANC. Shugaba Ramaphosa da jam'iyyar ba su wani katabus don magance harin da ake kai wa baki ba. Maimakon haka ya kara rura wutar ne don karkata hankalin jama'a daga matsaloli da kuma gazawar gwamnatinsa."

Duk da matsalolin da kasar ke ciki, masana sun yi hasashen cewa jam'iyyar ANC ce za ta lashe zaben na wannan Laraba.