1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe zagaye na biyu a Tunisiya

October 13, 2019

Ana gudanar da zabe a Tunisiya, zaben da al'umar kasar ke fatan ganin gagarumin sauyi a cikinsa ta fannoni da dama. Kasar dai na fama da matsalolin da ke bukatar shugaban da zai tabbatar da gyara.

https://p.dw.com/p/3RDYY
Tunesien Wahlen l Stichwahl um Präsidentenamt
Hoto: Reuters/Z. Souissi

A wannan Lahadin ne al'umar kasar Tunisiya ke zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda batun tsare dan takara Nabil Karoui ke ci gaba da zama abun muhawara, duk da cewar an sake shi ranar Larabar da ta gabata.

An dai kame shi tun da farko bayan sake bayyanar ayyukan ta'adda da aka alakanta da masu tsattsaurar ra'ayi.

Wanda ya yi nasara a zaben zai gaji matsalolin tattalin arziki da na rashin ayyukan yi  da yanda za a iya shawo kan rigingimun tsaro.

Galibin 'yan kasar dai na sa ran ganin sauyi cikin gaggawa daga halin da ake ciki a yanzun.